Tarurruka

Tun shekara ta 2011 muna aiki da bebaye da kurame a jihar Kano domin haɗa ƙamusan harshensu, wato harshen bebaye na ƙasar Hausa ko kuma maganar hannu. Kowane littafi ya ƙunshi kalmomin wani fanni dabam.

A tarurrukan da muka yi a shekarun baya domin shirya waɗannan littattafai, da bebaye da masu zane-zane sukan haɗu sai a tattauna kowace kalmar da za a saka cikin littafin a kuma zana ta. Ya zuwa yanzu mun haɗa littafi har guda tara.

Ana iya amfani da waɗannan littattafai domin koya wa bebaye karatu da rubutun Hausa. Littattafan ba na sayarwa ba ne, ana ba da su kyauta. Muna rarraba su a makarantun bebaye na yara na gwamnati da na masu zaman kansu, a azuzuwan Yaƙi da Jahilci na bebaye waɗanda aka kafa a shekarun baya, da kuma a ƙungiyoyin bebaye a arewacin Nijeriya.