Harshen bebaye na ƙasar Hausa

Maganar hannu, sunan da bebaye suka ba wa harshensu, harshen bebaye ne na ƙasar Hausa (“Hausa Sign Language” a Turance). Ba a san asalin harshen bebaye na ƙasar Hausa ba, amma ana kyautata zaton cewa tun lokacin da bebaye da kurame suka fara hulɗa da juna suna amfani da wannan yaren nasu.

Harshen bebaye na ƙasar Hausa yare ne cikakke mai zaman kansa, ya kuma bambanta da harshen Hausar baka ta yadda ake ƙirar kalma da kuma ta yadda ake ginin jumla, ma’ana tsarin sauti da nahawun harshen bebaye sun sha bamban da na Hausar baka. Amma da Hausar baka da al’adar Hausawa suna da tasiri a kan harshen bebaye.

Ba a koyar da harshen bebaye na ƙasar Hausa a makarantun bebaye. Yara sukan koyi yaren a wurin iyayensu, ko abokansu, ko ’yan ƙungiyar bebaye. Harshen bebaye ya kuma bunƙasa duk inda bebaye da kurame suke haɗuwa, ko a makarantunsu da azuzuwansu, ko kuma a ƙungiyoyinsu cikin gari da kuma ƙauyuka.

Download the dictionary or search for signs on this site:

Littattafai: Helmut Buske Verlag